Takaitaccen Tarihin Sheikh Abdallah Gadon KayaDaga Aliyu Shuaibu Aliyu

Takaitaccen Tarihin Sheikh Abdallah Gadon KayaDaga Aliyu Shuaibu Aliyu✍

Malam haifaffen garin Gombe ne (Kumo), Mahaifinsa kuma dan Giade ne (Bauchi) Shi ne farkon wanda ya kai Izala garin Giade. Daga baya karatu ya zaunar da Malam a Kano.Malam yayi karatu a Makarantar Legal ta Kano kafin tafiyar shi Madina.Hakanan, Malam yayi karatu a wurin Malamai da dama, ya kuma bi zaurukan Malamai ya dauki ilimi. Daga cikin Malaman shi akwai;– Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba (Rahimahulla).– Sheikh Abdulwahab Abdallah.– Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (Rahimahullah)– Sheikh Dr. Muhammad Sani R/Lemo.– Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar.– Sheikh Dr. Muhammad Sani B/Kudu da sauran su.Malam mahaddacin Alkur’ani ne, wanda Allah ya ba wa daddadan sautin karatun shi.Malam yaje Madina yayi karatu a Kulliyatul Hadis, kamar yadda ya bibiyi wasu daga cikin majalisan Malaman wannan gari ya kwankwadi ilimi daga gare su.Bayan dawowar Malam daga Madina, ya dora Masters a Jami’ar Bayero ta Kano.Malam yaje kasar Sudan inda ya yi PhD ɗin shi a can.Malam mutum ne me son ilimi da daliban ilimi, da kokarin karantar da shi. Kamar yadda Allah ya hore masa lafiyar fita yada da’awa a sassan wannan kasa da ma makotan kasashe.Malam mutum ne, me kyawawan dabi’u, wanda duk wanda ya zauna da shi zai fahimci haka. Ta yadda yake jan dalibansa a jiki sosai, da shiga cikin lamuran su.Malam Limami ne a Masallacin Usman Bn Affan Gadan Kaya.Kasancewar Malam karantarwa ya sa a gaba, hakan ta sa ya karantar da litattafai da dama a fannoni daban-daban, daga cikinsu akwai

hakan ta sa ya karantar da litattafai da dama a fannoni daban-daban, daga cikinsu akwa

1. Umdatul Ahkam

2. Bulugul Maram

3. Riyadus Salihin

4. Sunut Tirmizi

5. Iziyya

6. Risala

7. Addurratul Bahiyya

8. Waraqat

9. Alwadhih fi Usulul Fiqh

10. Alqawa’idul Fiqhiyya

11. Usulus salasa

12. Alkawa’idul Arba’a

13. Kitabut Tauhid

14. Usulus Sunna na Ahmad

15. Kashfusshubhat

16. Aqidutud Dahawiyya

17. Aqidutul Wasidiyya

18. Juz’ul Kira’a Khalfal Imam

19. Alfiyatus Suyudi ta hadisi

20. Alba’isul Hasis

21. Sharhus sunna na Barbahari

22. Alqawa’idul Musla

23. Kitabul kaba’ir

24. Muktasarus Sira

25. Tahzibus Sira na Nawawi

26. Arba’una Hadisan

27. Attabsira fi Ulumil Qur’an.

28. Hilyatu Dalibil ilmi

29. Ta’alimul Muta’allim

30. Usulus Sunna na Humaidiy

31. Sharhus sunna na Muzani

31. Aqidatud Raziyayn

32. Sarihus Sunna na Dabari

33. Qasidatul Ha’iyya

34. I’itiqad ahlis sunna na Isma’eeliy

35. Almanzumatur Ra’iyya

36. Al’iqtisad fil i’itiqad

37. Lum’atul I’itiqad

38. Almanzumatul Lamiyya

39. Al’aqidatus saffariniyy