Tirkashi Aminu Shariff Momo Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Yayiwa Umma Shehu Tambaya Akan Addini Ta Kasa Amsawa

Aminu Shareef momoh ya fadi dalilin da yasa yayiwa Umma shehu tambaya akan addini

Momon dai idan baku manta ba a kwanakin baya ne ya jawowa wannan jarumar sututu a idon duniya da mutane wasuma harda cewa ai Wannan jarumar jahila ce ba abinda ta iya daman maganganu dai marassa dadi kowa da irin yadda yake fada akan wa wannan jarumar wanda kuma hakan ba daidai bane saboda ba kowa ne aka haifeshi da iyawa ba.

Ba kowane wanda ya jawo mata wannan ba illa jarumi dan uwanta wato Aminu Sharif momo Wanda yake aiki a gidan television na arewa 24 wanda ananne yayi mata wannan tamabyar mai rikitarwa wanda kowa yasan bataji dadin taba.

Ya bayyana cewa ba komai ne yasa yayi mata wannan tambayar ba illa yaga cewa yan Film sune kashin bayan al’umma su ake kalla ayi wani abu wanda idan basu kasance suna da ilmi ba tome akayi kenan inji Aminu Sharif.

Sai abin tambaya me yasa bai taba yiwa kowa ba sai wannan jarumar kodai ita ya rana a kannywood ko kuma daman yasan cewa bata sani ba shi yasa yayi mata wannan tambayar shi kadai yasan wannan dalili wanda idan aka duba ta wani waje za’a ga yayi daidai ta wani wajen kuma za’a iya kalubalentar shi.

Allah dai ya kyau amma kuma wannan ba wata tambaya bace wacce za’a ce ta sha kan wannan jarumar matukar Mutum yayi makarantar Islamiyya to wannan amsa ce me sauki sai dai daman baiyiba