Tirkashi sadiya Haruna ta Fashe da kuka bayan anyi mata kyautar mota

Tirkashi sadiya Haruna ta Fashe da kuka bayan anyi mata kyautar mota

Sadiya Haruna wacce ake kira da sayyada sadiya Haruna wato wacce da take yabon Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam daga bisani kuma ta rikide ta koma wata harkar daban wanda ba haka aka so ba kuma itama batajin dadin irin kallon da mutane suke mata a yanzu saboda taje gidan maza ta dawo.

Ta cikin wani sabon video wanda itace ta wallata wannan bidiyon da hannunta kuma mutane sunyi matukar mamaki ganin yadda aka ganta tana shekar kukanta saboda tsabar farin ciki da kuma murna wanda kowa da yadda yake iya nuna nasa farin cikin.

Ta bayyana farin cikinta inda take godiya ga wani babban uban gidanta wanda ya gwangwajeta da kyautar sabuwar mota wanda hakan yasa ta ta shiga shauki wanda har kuka tayi bata sani ba tsabar murna.

Sai dai wasu kuma suna kalubalentar wannan matar saboda wannan motar da aka bata motace mai matukar tsada wanda Acikin maza ma ba kowa yake iya siyan wannan motar Ba amma ita kuma a banza ma ta sake ta shine wasu ke ganin kamar kudi tasa ta siya bawai kyauta aka bataba

Sai dai kuma da yawa daga cikin masoyan wannan jarumar sun jinjina mata saboda yadda take zaune da kowa lafiya wanda shine ma abinda yasa ta samu kyautar wannan motar