Tunda nake fim ba’a taba biyana dubu 200 ba sai Mai Shadda cewar Shuaibu Lawan Kumurci

Fitaccen jarumin Kannywood wanda yaga jiya kuma yake ganin yau Shu’aibu Lawan Kumurci yayi wata magana wacce ta dauki hankalin mutane sosai matuka gaya.

Jarumin ga wadanda suke bibiyar Al’amuran masana’antar yana daya daga cikin jarumai da sukayi shura wajen fitowa a shigar Daba ko kuma Fashi da makami ko kuma duk wani nau’in lefi a finafinan Hausa.

Jarumin ya bada gudunmawa sosai wacce bazata misaltu ba.

Sai dai kash! Inda gizo ke sakar Jarumin a yau ya fito ya bayyana duniya irin jin dadin da yayi da aka dauki dubu 200 aka bashi a matsayin kudin daukar shiri mai dogon zango na Dan Jarida da suke dauka na kamfanin Abubakar Bashir Mai Shadda.

Sai dai mutane da dama sunyi mamakin fadin hakan daga bakin sa domin tambayar da take zuwa bakin masoyan itace; Shin a Ina sauran matan da wasu Jaruman suke samun kudaden shiga har suke yin rayuwa ta Alfarma da Dagawa?

Zamu so ku bayyana mana ra’ayoyin ku akan wannan labarin.