Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, ta yi Allah-wadai da kisan gillar da wasu masu tsattsauran ra’ayin addini suka yi wa mahauci Usman Buda a jihar Sokoto.
KU KARANTA KUMA: Zulum Yayi Allah Wadai Da Kisan Wasu Manoma 8 Da Mayakan ISWAP Suka Yi A Borno
Kungiyar kiristoci ta mika ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da kuma wadanda suka san shi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kiristoci Daniel Okoh ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Abuja ranar Alhamis.
Rahotanni da dama na nuni da cewa an kashe Usman Buda da wulakanci a kan wani kalami na batanci.
KU KARANTA KUMA: Emefiele Ya Lalata Kudin Najeriya – Tinubu
Kungiyar ta CAN ta bayyana cewa tana matukar goyon bayan ‘yancin addini da fadin gaskiya cikin lumana, kuma ta yi Allah wadai da duk wani nau’i na tashin hankali ko kuma adalci na kabilanci da ake yi da sunan addini.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Wannan mummunan lamari yana kara nuna bukatar kara kaimi wajen samar da juriya da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummarmu.”
Kungiyar ta CAN ta bayyana cewa, za ta ci gaba da bayar da shawarwarin kare hakkin dukkan ‘yan kasa, ba tare da la’akari da addininsu ba.
KU KARANTA KUMA: Abin Dariya Ne A Ce Buhari Ya Mutu – Obasanjo [VIDEO]
Sanarwar ta kara da cewa “Muna kira ga malaman addini da mabiya da su inganta tattaunawa tsakanin addinai da kuma zaman lafiya a Najeriya.”
A wannan mawuyacin lokaci dangin Usman Buda suna cikin tunani da addu’o’inmu.
Leave a Reply