Uwar Da Aka Kamata Da Saurayin ‘Yarta Suna Lalata Tayi Bayani

Idan masu karatu basu manta ba, mun kawo muku labarin wata uwar data yi abun kunya inda ‘yar Cikinta ta kama saurayinta akan ruwan cikin Mahaifiyarta, to ita uwar ta yi bayanin yadda abun ya faru.


Tace, “tabbas na biyewa raina, amma a gaskiya ina kaunar saurayin ‘yata tun ranar da ta soma kawo mini shi a matsayin wanda zai aureta, tun daga wannan ranar raina ya kasa hakura akansa”. Inji uwar Yar.

Taci gaba da cewa, ” Na yanke shawaran na yaudareshi ne domin na haramta masa auren ‘yata. Hakan yasa na bar kofar dakin a bude yadda zata ganmu. Sai dai ba kamar yadda ita ta fadawa duniya ba wai ta kamamu turmi da tabarya. Ban yi zina da shi. Ta dai ganshi a tube babu komai a jikinsa sai karamin wandonsa. Ni kuma na daura zani a kirji wannan yasa ta yanke hukuncin zina muke yi”.

Sai da uwar tace ta rarrashi yar tata daga baya kuma ta fadamata gaskiyar abunda ke ranta na ta bar mata saurayin nata ita ta aureshi.

Sai dai mai tsaigunta mana labarin bai samu bayanin ko diyar ta yarda ta barwa uwar tata ko kuma har yanzu tana son kayanta ba.

News All.