Video yadda yan ta’adda suka dinga azabtar wadanda suka sace a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja

Ajiya rudunar Yan Ta’addan da suka sace mutanen Jirgin kasa na hanyar Kaduna Zuwa Abuja, sun saki Wani bidiyo Wanda ke nuna yadda suke zane wayandda sukayi Garkuwa Dasu.

 

A cikin bidiyon, ’yan ta’addan sun kuma yi bugun kirjin cewa za su ruguza kasar nan, sannan za su kashe wasu daga cikin fasinjojin da ke hannunsu su kuma sayar da sauran.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa, idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.

Bidiyon kwata kwata babu kyawun gani, ganin yadda Yan uwanmu ke ihu suna neman taimako.

https://youtu.be/6yHroO2geOg