Wani Dan Najeriya yayi wuff da wata kyakkyawar baturiya, bidiyon yadda take masa hidima ya dauki hankula


Wani matashi dan Najeriya mai amfani da @kanorsamuel223 a manjajar TikTok ya saka wani bidiyon budurwar sa Baturiya a kafar.

Wani bangare na daga cikin bidiyon ya nuna kyakkyawar baturiyar na amfani da tukunyar gas tana soya masa filanten. Ta nuna cewa lallai ita fa taga wurin zama.

Matashin ya samu kyakkyawar baturiya

Idan da ba domin yanayin kalar fatar jikinta ba, da sai ayi tunanin cewa ‘yar Najeriya ce bisa yadda take gudanar da dafa abincin.

Mutane da dama sun yi tururuwa zuwa bangaren yin sharhi domin tambayar matashin yadda akayi ya samu wannan kyakkyawar baturiyar a matsayin budurwar sa.

Ku kalla bidiyon a nan.

Bidiyon ya dauki hankula sosai

Akwai akalla sama da mutum 400 da suka yi sharhi a kan bidiyon, yayin da sama da mutum dubu sha bakwai suka danna alamar so akan bidiyon.

Alex George ya rubuta:

“Pablo kayi kokari, lokacin ka ne na tunawa cewa lallai akwai so na gaskiya, ‘yan’uwanta kar mu yasa nace maka nagode.”

halo ya rubuta:

“Dan’uwa ya samu nasara a rayuwa!!! yooooooooo!”

Dandy McCarthy ya ributa:

“Surkullenka mai karfi ne.”

Tik Toker ya rubuta:

“Ya samu katin zama dan kasa.”

washy ya rubuta:

“Har yanzu ina ta tunanin abinda za a samar.”