Wani dan Nigeria ya kera mota irinta ta farko a duniya me amfani da hasken rana

Wani dan Nigeria ya kera mota irinta ta farko a duniya me amfani da hasken rana,

Dan Nigeria mai suna Mustapha Gajibo daga jihar Borno ya kera mota mai cin mutum goma sha biyu (12) irinta ta farko a duniya mai amfani da hasken rana sannan kuma tana amfani da wutar lantarki.

Motar dai tana da abubuwa kamar haka:

Abubuwan da kunsa: kujera 12, zata iya tafiyar kilo mita 212 (212km) idan aka yi mata caji É—aya, sanna tana tafiyar 110km a duk awa daya, cikakken kwandishan, tsarin umarnin murya, yadda zaka iya bata umarni abu.

Tuni dai ya gabatar da wannan motar ga ga masana don kara yi mata binciken kwakwaf wanda suka tabbatar da ingancinta.