WANI LAUYA YA YIWA PROF MAQARI WANKIN BABBAN BARGO

WANI LAUYA YA YIWA PROF MAQARI WANKIN BABBAN BARGO.

Wani fitaccen Lauya a Jihar Kaduna Barister Aliyu Yahaya Husain,ya yiwa farfesa Makari wankin babban bargo akan maganarsa da yayi game da yajin Aikin Asuu,inda lauyan yakira maganganun farfesan a zaman Tsantsar Son zuciya.

Ga abunda ya ce:

Ba iya rashin adalci bane a maganar Professor Maqari ba, harda son zuciya da zubar da kimar jami’ar Bayero.

A matsayin shi na Malamin jami’a wanda ya taka matakin karshe a koyarwa, duk abinda ya faɗa akan Malama jami’a madubi ne dake haska kan shi; bayani ne akan waye shi.

Malaman Jami’a basa research, eh mana! Toh dame zasu yi research ɗin?
Wa ke ɗaukar nauyin research ɗin?
Ashe ba harda rashin biyan EAA (earned academic allowance) yasa Malaman jami’a yajin aiki ba ? Neman promotion ai ya zama dole ga ma’aikaci.

Akwai Malaman da nasan da kuɗin aljihun su da gwagwarmayar shiga nan fita nan suke funding research a jami’o’i saboda sha’awa ba don Gomnatin ƙasarmu yar goyo ce ba. Allah ya jiƙan Professor Malumfashi Ibrahim ba don ya mutu ba.

Ashe ba anan facebook kwanakin baya naji wani Malamin jami’a Abdelghaffar Amoka yana kukan yadda yake fama da research da yunkurin kafa wani dakin bincike a jami’ar Ahmadu Bello ba ? Gomnati ke biyan shi? Kowane Malami keda irin wannan energy? A’a!

Duk abinda Malam Prof. Ibrahim Maqari ya zayyana zamu ɗauka yana magana ne from experience wanda hakan shine silar taɓuwar mutumcin Jami’ar Bayero.

*Wanke takardu don zama Farfesa
*Rashin Research
* Koyarwarwa tsahon shekaru da handout ɗaya ba update.

Duk ba wannan ba, Malam yana magana ne akan yasan abinda yake faruwa, yasan maƙasudin yajin aikin, kuma yasan me Malaman suke yiwa, ya kuma ya ɓuge da caccakar malaman da kuma condemning jami’o’i gaba ɗaya, haba!

Akwai abubuwan da Malam ya faɗa gaskiya ne, eh, amma me ya kawo su, ko kuma mene ya haifar da su ?
Malam yabi ta ɓarawo, be damu da mabi sahu ba.
Ya bugi jaki, ba ruwan shi da taiki.

Ya kamata ayi ma Malamai adalci. Ko da suna da laifi, laifin Gomnatin ƙasarmu yafi yawa.

In Gomnatin taga dama, zata gyara, kuma komai ze yi dai-dai, Malaman mu a shirye suke.

Allah yasa mu dace.