Wani mutum ya yanke golayensa yana bacci a Ghana

Wani manomi a Ghana yana can kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marenansa (golaye ko kwalatai) a lokacin da yake barci.

Mutumin mai suna Kofi Atta, wanda a gadon asibitin da yake ya gaya wa BBC yadda lamarin ya faru, yana can ana ƙoƙarin duba yadda za a yi masa aiki.

Ya ce a yanzu dai ana sa masa ƙarin ruwa ne tare da wasu allurai da ake ta yi masa, amma dai sai an yi masa tiyata.

Sai dai ya ƙara da cewa a yanzu ba shi da ko kudin da zai biya motar asibitin da za ta dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a kasar ta Ghana inda a can ne za a iya yi masa tiyata. 

Mutumin ya ce, yana barci ne na ƙailula wato da rana a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama da ke ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marenan nasa.

Mista Atta ya ce abin ya ba shi mamaki ƙwarai domin har lokacin da wasu maƙwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya riƙa jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.