Wata amarya ta shiga tashin hankali bayan ta gano cewa angon data aura bakanike ne ba dilan motoci ba

Wata budurwa ta bayyana yadda kawarta ta gano asalin sana’ar mijinta bayan an daura musu aure a shafinta na kafar sada zumuntar zamani taTwitter, kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka ruwaito.

Kawar amaryar mai amfani da suna agneeess ta nemi shawarar jama’a akan abinda ya dace ayi tunda ba a kammala shagulgulan daurin auren ba.

Kamar yadda amaryar ta bayyana a shafin nata na sada zumunta Twitter:

Kawata ta gano cewa, angonta bakanike ne ba dilan motoci ba bayan an daura musu aure.

Ya kuke ganin ya dace tayi ? Abin lura anan shi ne ba a kammala liyafar auren ba.