Wata Kishiya Ta Halaka Amarya A Ranar Daurin Aurenta A Sokoto

Wani lamari me cike da sarkakiya wanda ake zargin kishiya da kisan amarya a ranar daurin ta a Sokoto.

Labarin da muka samu daga majiyoyi da dama na nuni da cewa Allah ya karbi ran wata amarya a garin Sokoto dake a arewa maso yammacin Najeriya a ranar daurin auren ta.

Kamar dai yadda rahotannin na mu suka nuna amaryar ta fadi ne kasa kawai ta mutu a sakamakon wani matsanancin ciwon kai da ta ce tana fama da shi jim kadan bayan ai gama daurin aure kuma ana shirin tafiya kaita dakin ta.

Amihad.com ta samu cewa bayan an kammala daurin aure da safe, lokacin da ango ya turo motoci domin a daukar masa ita sai amarya ta bayyana masu cewa kanta na matsanancin ciwo sosai don haka a dakata.

Kamar ba za a dakata ba, amma ganin yadda ta matsa har da kuka akan ciwon kan nata sai aka bukaci a jira zuwa mintuna talatin a ga ya za a yi ko ciwon kan zai sassauta amma sai Allah ya karbi abun sa.

Tuni dai mutane suka fara zargin kishiyar da kisan inda suka ce daman can uwar gidan bata so auren ba.

Da Kudin Ajo Na Biya Wa Kanwata Kudin Makaranta – Wata ‘Yar Dirama

Kazalika mun samu zantawa da daya daga cikin ‘yammatan gidan, da ta yi magana da yawun shugabar ‘yammatan gidan, bayan da muka nemi jin ta bakin shugabar matan amma ba mu same ta ba, ta bayyana mana sunanta da abin da ya fito da ita daga gida, inda ta ce ta ji sha’awar wannan sana’a ce ta hanyar wata kawarta da suka hadu a shafin sada zumunta na Faccebook.

A ta bakinta…
Sunana Karima Bala daga Gwagwalada, kawai gani na yi wannan sana’a ta ban sha’awa, amma ba don na rasa ci da sha da sutura a gidammu bane. Kawai dai ina sha’ar abin ne idan na zo kallo, don haka sai abin ya ban sha’awa kawai ina son wasan a rayuwata.

Ba saboda auren dole ta bar gidansu ba…
Ni dai ba a taba cewa za a yi min aure ba ballantana na gudu, kuma harkar makaranta babana yana kokari, kawai dai na yi sha’a ce saboda na hadu da aboki a shafin sadarwar zamani, to muna hira da ita sai ta nuna min yanayin harkar da take yi.

Da farko dai ban gaya wa iyayena inda zan ce na ce musu dai zan je makaranta sai na taho wurinta.

Da na zo na yi wasa na kamar sati daya ban koma gida ba, an nemi ba a ganni ba, daga baya aka gano inda nake aka zo aka mayar da ni gida.
Yanzu dai ina da kyakkyawar fahimtar juna ni da iyayena, idan zan zo nan sai in ce mata Momcy ina son zuwa gidan Dirama kuma na taho.