Wata mata ta yankewa bazawarinta mazakuta bisa yunkurin yiwa yarta fyade

Wata mata mai shekara 36 a duniya, ta yanke mazakutar saurayin ta mai shekara 32 a duniya, da wuƙa bisa zargin ƙoƙarin yiwa ɗiyarta mai shekara 14 a duniya fyaɗe.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa lamarin ya auku ne a yankin Lakhimpur Kheri, a jihar Uttar Pradesh ta ƙasar Indiya.

Tare matar da saurayin suke rayuwa

A cewar jami’ai, matar da ƴar ta suna rayuwa tare da mutumin na tsawon shekara 2 bayan ta rabu da tsohon mijinta mai shan giya.

Matar wacce ta shaidawa Times of India cewa tana aiki ne a gona lokacin da lamarin ya auku.

Tayi iƙirarin cewa ta isa gida akan lokaci inda ta kama saurayin nata dumu-dumu yana ƙokarin yin fƴaɗe ga ɗiyar ta.
Matar ta kuma ce ita ma yayi ƙoƙarin kai mata hari.

Ina ƙoƙarin ceto ƴa ta ne kawai sai hannu na ya kai kan wuƙa na yanke masa mazakuta domin na koya masa hankali. Ko kaɗan ban yi nadamar abinda na aikata ba.

Hukumomi sun yi ƙarin haske kan lamarin

A cewar jami’in SHO na ofishin yan sandan Lakhimpur, an saka saurayin cikin jerin masu aikata fyaɗe a bisa dokar POCSO.

SHO ɗin ya kuma ƙara cewa wanda ake zargin yana cikin matsanancin halin da ƙila sai an kai shi zuwa birnin Lucknow domin cigaba da duba lafiyar sa.

Har yanzu dai ba a sani ba ko za a tuhumi matar bisa laifin yankewa saurayin nata mazakuta.