Hukumar ƴan sandan jihar Kebbi ta cafke wata matar aure mai shekara 30 a duniya, Farida Abubakar, bisa zargin sa hannun ta a kisan mijinta, Attahiru Ibrahim Zagga.
Shafin Linda Ikeji ya ambato kakakin hukumar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a 26 ga watan Agusta.
An cakawa mamacin wuƙa wacce tayi sanadiyyar rasuwar sa
Kakakin yace Attahiru Ibrahim, wanda alƙalin majistare ne a jihar Kebbi, an caka masa wuƙa har ya mutu a gidan sa dake cikin Birnin Kebbi a daren ranar Alhamis.
A ranar 25/8/2022 da misalin ƙarfe 11:40 na dare, jami’an ƴan sanda dake a Gwadangaji, sun samu bayanin cewa anji wata baƙuwar ƙara a gidan wani makwabci, mai suna Attahiru Ibrahim, na kwatas ɗin Alieru, a Birnin Kebbi, sannan kofar gidansa a kulle take. A cewar sanarwar
Bayan samun bayanan, an tura jami’an ƴan sanda cikin gaggawa zuwa gidan inda suka shiga da ƙarfin tuwo, sannan suka tsinci Attahiru Ibrahim kwance cikin jini, wanda daga baya likita ya tabbatar da rasuwar sa
Ana zargin matar auren da aikata kisan
Haka kuma, matar sa mai suna Farida Abubakar an ganta a cikin gidan. Hakan yasa ake zargin ta sannan aka cafke domin bincike kan lamarin.
A halin da ake ciki, kwamishinan ƴan sandan jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora, ya bayar da umurnin tura lamarin zuwa ɓangaren SCID, Birnin Kebbi, domin gudanar da sahihin bincike wurin binciko gaskiyar lamari dangane da wannan mummunan lamarin.
Wani abokin mamacin mai suna Aminu Ubandoma ya tabbatar da rasuwar sa a wani rubutu da yayi a shafin sa na Facebook.

Leave a Reply