Yadda aka kama dan sanda yayi wa ‘yar kanwar sa ciki

Wata rundunar yan sanda a najeriya sunyi nasarar kama wani ma’aikacin su wanda yayi wa ‘yar kanwar sa ciki a jihar nasarawa, yarinya ce yar kimanin shekara sha shida wacce yayi wa cikin shegen.

Daga baya da aka kama shi an kara kamo wasu mutane ukku wanda su ma suna daga cikin wadanda akayi wannan mummunan aiki dasu.

A wani rahoto da muke samu kungiyar mata ta najeriya wato (FIDA) tace baza tayi kasa a guiwa ba wajen gano gaskiyar lamarin sannan su hukunta duk wanda yake da hannun akan wannan mummunan aiki.

A wasu bayanai da 24blog ta samu a garin da wannan lamari ya faru, yan sandan wannan gari sun yi nasarar kama duk wani wanda ake zaegin yana da hannu akan wannan mummunan aiki.

Kungiyar (FIDA) ta bayyana sun dade da samun rahoto a wajen wata kungiya ta garin da wannan lamari ya faru wannan kungiya ta bayyana masu abubuwan da suka sani akan wannan lamari.

Suka ce “bayan mun samu wannan labari da hujjoji ba muyi kasa a guiwa ba muka je muka kama wannan dan sanda tare da iyalen sa.

“Sannan muka yi saurin tafiya da yarinyar asibiti domin ayi mata gwaje-gwaje bayan sakamakon gwaji ya fito muka gane cewa tana da ciki har ya kai wata shida kuma an yi kokarin zubar dashi Allah bai so ba.

Bayan wasu yan kwanaki yarinyar ta haihu amma yaron yazo babu rai saboda ya mutu tun a ciki dalilin kokarin zubar da cikin da akayi.

Bayan tambayoyi da akayi wa yarinyar ta bayyana wa yan sanda cewa tabbas shins yayi mata ciki domin kullum idan ya dawo gida yana kawo mata kayan kwadayi tana sha sai ta kama bacci idan ta farka sai taga jini a jikin ta.

A yadda ta bayyana sai daga baya ta fahimta abinda yake faruwa da ita sannan ta gano kawun tane yake amfani da ita.

Kungiyar kare hakkin mata wato (FIDA) tayi alkawarin hukunta wannan dan sanda da sauran masu hannu akan wannan lamari.