Yadda aka tsinci gawar wani mutum a kwata a jahar kano

An tsinci gawar wani matashi mai kimanin shekaru 25 mai suna Ghaddafi Saleh a cikin wata kwata da safiyar Laraba a Jihar Kano.

Lamarin dai ya faru kan titin unguwar Kundila.

A zantawar Aminiya da wani matashi kuma mazaunin yankin, Sultan Bello, ya ce ruwa ne ya koro gawar mutumin ya kawo ta wannan waje.

Ya kuma ce, “Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake tsintar irin wannan gawar, na uku ke nan cikin kwanaki hudu da suka wuce.”

A nasa bangaren, mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano,