Yadda Ake Kara Kugu (Hips) Da Karin Ni’imar Mace

Yadda Ake Kara Kugu (Hips) Da Karin Ni’imar Mace

Yan uwa mata na yawan kokawa kan yadda wasu mazan basu damu da su ba, balle su biya musu hakikanin ibadar aure yadda ya kamata.

Wasu kuma suna korafin wai mazajen nasu na kokawa kan basu da ni’ima a jiki, ma’ana basa jin komai daga gare su.

KARIN KUGU HIPS NA MACE

Masu neman karin hips inaso a fahimci cewa girman kigu halitta ce, wasu matan har kauce hanya sukeyi,su je a saka musu kugun roba kunga akwai alamar kauce hanya a nan kenan akwai nau’in ababen da mace zata rika ci.

Sannun a hankali, kyan diri da halittarta zasu kara fitowa, ita ma zata rika ji ta kara cika, tayi kyau, masanan a wannan fannin, sun bayar da shawarwarin.

Amfani da;

Abarba

Ayaba

Gwanda

Kankana

Zuma

Madarar ruwa

A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a dan kara zuma da madara bayan wannan, mace za ta rika hada da ganyen.

Alayahu

Tumatiri

Albasa

Ki yi kwadonsu ki rika ci haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai, insha Allah.

KARIN NI’IMAR MACE

Dangane da bayani kan abubuwan ni’ima kamar kullum mukan bayyana cewa a yawaita samun:

Ruwan rake

Ruwan kankana

Ruwan kwakwa

Sai a matse su, a hade ruwan guda, ki rika sha so uku-uku.

A rana uwargida,kina iya yin wani hadi na musamman, wanda shi kansa maigida zai iya amfani da shi, hakan ma yana kara dankon soyayya da fahimtar juna.

Misali:

Alkama

Danyar gyada

Waken soya

Aya

Madarar ruwa.

Sai ki jika ki markada su, ki tace, idan ya zama gasara sai ki rika damawa kamar yadda ake dama koko, sai ki zuba madara ta ruwa, kiyi kamar sati biyu kuna sha, da yarda Allah za a dace.