Yadda azaba ta komadar da sojan Ukraine bayan kwashe watanni 4 tsare a Rasha

Hoton wani sojan kasar Ukraine ya bayyana a shafukan sada zumuntar zamani wanda hakan ya girgiza zukatan jama’a da dama kamar yadda Instablog9ja ta ruwaito.

A wani hoto wanda mutane da dama jikinsu yayi sanyi an ga yadda ya karmashe ya lalace bayan kwashe watanni 4 a tsare.

Shafin Defense of Ukraine ne ya wallafa inda ya bayyana cewa:

“Sojan kasar Ukraine, Mykhailo Dianov yana cikin sojoji masu nasarar da su ka iya jurewa kuma da ransu yayin da Rasha ta kama su ta tsare. Wannan abin ban tausayi ne.”

Nan da nan mutane su ka dinga tsokaci iri-iri dangane da yadda halittarsa ta sauya. Wasu su na ganin bakar azaba da rashin cin abinci ne ya mayar da shi haka.