Yadda Daga Karshe Umar M Shareef Ya Bayyanawa Duniya Matar Shi Bayan Shekara Goma Da Aurensu

Duk wani bahaushe wanda ya mallaki hankalinsa kuma ma’aboci sauraron wakoki koda bana hausa yake j ba yasan mawaki Umar M Shareef saboda yayi suna matuka kuma yana daya daga cikin manyan mawakan hausa a najeriya wanda yaci zamani kala kala kuma haryanzu ana gwabzawa dashi.

Wannan mawaki yana daya daga cikin mawaka da jaruman da ake ganinsa da cikar kamala da nutsuwa saboda baitaba nuna wata rayuwarshi wacce take bukatar a sirrinta taba a soshiyal midiya. Mutane suna matukar yabon shi a duk lokacin da aka zo wajeb maganar bayyana iyali a kafafen sada zumunta.

Babu wani mutum wanda yasan matar wannan jarumi sai bayan da sukayi shekaru goma da aure sannan ya bayyana wannan hotuna nasu tare da ita. Mutane da yawa sunji dadin ganin matarsa kamar yadda suke ta korafin basu santa ba amma sun san yayi aure.

Wasu kuma sunyu bakin cikin bayyana matar shi da yayi wanda ya karya shedar da sukeyi mashi amma duk da haka wasu daga ciki sun taya shi murna domin ganin irin cikin farin ciki da suke da soyayya sannan da shakuwa da juna. Mutane da yawa sunyi masu fatan alheri.

Allah ya kara masu zaman lafiya mai dorewa. Ameen.