Yadda Mata Ta Haifo Yaro Ba Tare Da Ta Saduwa Da Namiji Ba

Wata mata mai suna Aba tayi ikirarin cewa ta dauka ciki kuma ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.

Yayin zantawa da Barima Kaakyire Agyemang a step 1 TV, Aba tayi ikirarin cewa shekara hudu rabonta da kwanciya da namiji.

Kamar yadda tace, lokacin da ta fara fuskantar wani irin ciwon ciki da kumburi, tace tayi tunanin cutar fibroid ce.

Bayan isarta asibiti, tayi ikirarin cewa an sanar da ita ta shirya za a yi mata aiki domin cire abinda ke cikinta, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Ta kara da cewa, ta yi kokarin yin mishi domin cutar fibroid din ta fita ba tare da an tsaga ta da wukar likita ba, amma abun mamaki sai santalelen yaro namiji ya fado.

Mahaifiyar jinjirin wacce ke siyar da ruwa a bakin titi, ta kara da cewa bata da halin kula da yaron.

Ta bayyana yadda wata matar fasto ke kula da ita tare da jaririnta.

News All