Wani magidanci mai suna Abdulwaheed Lamidi mai shekaru 55 ya mutu a lokacin da yake tare da budurwarsa a hotal din ‘City International Motel’, dake wajejen matsayar motoci na Council Bus-Stop, a unguwar Ikotun ta jihar Legas.
Jaridar PUNCH ta tattara bayanan cewa, Lamidi din, da masoyiyar sa mai shekaru 32 sun hadu ne a yanar gizo, kuma bayan tattaunawa da junan su, sun amince su kulla soyayya.
So ya kankama har sun shirya haduwa a zahiri
Dangantaka ta yi karfi, inda masoyan suka yanke shawarar haduwa a fili.
Wakilin jaridar PUNCH ya samu labarin cewa, matar a ranar Asabar din da ta gabata ta yi tattaki daga gidanta da ke wata jiha domin ta gana da Lamidi din a hotal.
An ce masoyan sun kwana tare a daki. Inda washe garin Lahadi kuma, suka tashi da wani lamari daban
Wata majiyar ta ce, masoyan na cikin daki ne sai budurwar ta fito da gudu domin neman agaji.
Ya kara da cewa, a lokacin da wasu ma’aikatan hotel din suka shiga dakin, sai suka tarar da Lamidi a kwance baya motsi.
Budurwar ta ce, mutumin ya zo shiga bandaki ne, sai kawai ya zube ya fadi kasa. An kira wani likita da ke aiki a wani asibiti kusa da hotal din, lokacin da likitan ya isa dakin, ya tabbatar da cewa mutumin ya mutu.
Ta taho da nufin aure amma kuma mijin ya mutu
Budurwar ta kara da cewa, ta zo Legas ne domin ganawa da mutumin kamar yadda ya yi alkawarin zai aure ta. Inda ta taho da wasu kayanta, da niyyar zuwa gidansa a matsayin zama matar sa.
Amma maimakon su je gidan mutumin, sai suka tafi hotal din. Wanda suna cikin daki ne, sai ta fito da gudu ta nemi taimakosaboda faduwar mutumin .
Isowar mutane ke da wuya, sai suka ruga cikin dakin, inda suka same shi kwance a sume a kasa.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:40 na safiyar Lahadi amma yarinyar ta zo daga wata jihar ne a ranar Asabar.
Budurwar ta bayyana cewa,
“ta hadu da mutumin ne a yanar gizo, daga nan suka ci gaba da tuntubar juna ”
a cewar majiyar.
An kai gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki, yayin da aka kama matar domin yi mata tambayoyi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wacce ake zargin ta ki yarda a shigar da iyayenta cikin binciken.
Ya kara da cewa ,
“Mun tuntubi iyalan mamacin kuma sun bayyana mana cewa su gawar dan uwan su kadai suke da bukata ba wani bincike ba. Sun ce ba su da sha’awar gudanar da wani bincike. Amma har yanzu rundunar tana nazarin bukatarsu, wanda jami’an mu masu nazarin doka suke gudanarwa.”

Leave a Reply