Yadda Wata Amarya Ta Kulle Angonta A Bandaki Dan Hanashi Jin Dadin Daren Farko

Wani ango ne bayan an kai amarya an yi musu huduba kowa ya watse an bar ango da amarya bayan sun yi sallah sun ci abinci, sai ango ya ce wa amarya bari in je in watsa ruwa in dawo nan take amarya ta rakoshi har kofar Daki.

Bayan ango ya gama wanka ya zo zai bude kofa sai ya ji an kulle kofar, ashe amarya ce ta kulle shi ta baya.

Ko da ango ya ga haka sai ya kira Sunan amaryar ta zo don ta budeshi amma Amarya ta na ji kawai ta yi kwanciyarta ta Kyale ango a kulle cikin Toilet.

A haka dai Ango ya hakura ya samu wuri ya kwanta cikin Toilet har gari ya Waye.

Da safe Amarya ta taso ta bude ango ta Durkusa ta gaishe shi ta fara bashi Hakuri Kamar haka : ↓

ka yi Hakuri angona Lallai na san cewa ban kyauta ma ka ba Dalili kuwa shi ne na yi wa tsohon saurayina alkawarin duk wanda na aura a daren farkonmu a Toilet zan barshi ya Kwana, kuma Alhamdulillah!!! Na Cika alkawarin da na Dauka”.

Tofa!!!

Wai Idan Kai ne Angon ya zaka yi???

Ke Mace ce, Shin Wannan Amaryar ta Kyauta?