Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta wa Mazauna yankin Katsina don yin lalata da matan su da ‘ya’yan su

A wata hira da BBC Hausa ta yi da Dr Bashir Kurfi, shugaban yankin ya ce kauyukan Batsari, Dutsenma, Kankiya, Chiranci, Funtua, Safana, da dai sauransu a cikin Katsina, suna fuskantar hare-hare.
Kurfi ya ce ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun mamaye wasu kauyuka, yayin da mazauna garin ke neman mafaka a wasu wurare.

“A cikin ƙauyuka kuma ‘yan fashin suna kiran mazauna yankin su kawo musu matansu, ‘ya’yansu ko kannen su dan su yi lalata da su.
Baya ga hare-hare da kashe-kashen mutanen da basu ji ba ba su gani ba, suna kuma yi wa mata fyade. Na san wata mata da ‘yan bindiga sama da 40 suka yi wa fyade. Makarantu da yawa da aka rufe saboda ‘yan fashi sun zama gidan ‘yan fashi; kuma a wasu kauyukan tuni mutane na zaune tare da barayi a gidajensu.

‘Yan bindiga sun kwace gonakin mutane da karfin tsiyasukn mayar da jama’a bayi suna tilasta musu su yi musu noma, suna kuma yi wa ‘ya’yansu mata fyade,” inji shi.

Ya zargi gwamnati in da ya ce ba ta yi wani tanadi ga wadanda abin ya shafa ko taimaka musu don rage radadin halin da suke ciki ba.

Ya ce rashin tsaro da ake fama da shi a yankin ya sauya al’amura, inda ya ce a da a kullum motoci tsakanin 20 zuwa 50 ne ke zuwa Kano daga Sakkwato ko makwaftan garuruwa, amma hakan ya faskara saboda hadarin da ke tattare da hanyoyin.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani Dan achaba a jihar Osun

Wasu ‘yan bindiga a ranar Juma’a sun kashe wanidian achaba mai suna Toyin Oluwaseun, a cikin wani kangon gini a garin Ilesa na jihar Osun.

Har yanzu babu cikakken bayani ga me da lamarin sai dai wani mazaunin unguwar da ya so a sakaya sunansa ya ce ‘yan sanda sun tafi da gawar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yemini Opalola, a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ta bayyana cewa ‘yan sanda sun fara farautar wadanda suka aikata wannan aika aika, inda ta ce an ajiye gawar a dakin ajiyar gawa na Asibitin Wesley da ke Ilesa, domin a gwada gawar.
Ana ci gaba da bincike don ganowa tare da kama wadanda suka aikata laifin. Za a sanar da abinda sakamako ya fitar game da binciken”in ji Misis Opalola.
Ta ce ‘yan sandan sun samu labarin mutuwar mai babur din ne a lokacin da wani mai suna Taiwo Asa mamallakin wannan kangon gini ya kawo rahoton cewa ya tsinci gawar wani da bai san ko waye ba.