Yadda Yar Kasar Rasha Ta Kusa Halaka Kanta Don Burge Masoyanta A Instagram Da Hotunan4

Yanzunan Muka Sami Wani Labari Mai Ban Al’ajabi Ta Yadda Wata Budurwa Ta Kusa Halaka Kanta Kamar Yadda Shafin Labaran Hausa Suka Rawaito

Wata tauraruwa a kasar Dubai amma ƴar asalin ƙasar Rasha, Viki Odintcova mai shekaru 23 ta raɓa saman bene yayin da abokinta namiji ya riƙe hannunta yayin da take lilo a bene hawa na 1,004, Sahafin USA Today ne ya ruwaito.

Tauraruwar ‘yar kasar Rasha ta yanke shawarar daukar hoto wanda zai yi matukar daukar hankalin jama’a yayin da take lilo a babban bene na Dubai.

An dauki bidiyon nata ne sannan ta daura shi a Instagram yayin da wani namiji yake riƙe da hannun Viki Odintcova a benen.

Hoton ya dauki hankulan dubbannin jama’a a Instagram akan yadda ta kusa sadaukar da rayuwarta akanshi, mutane sun yi matukar mamaki.

Cayan Group, wadanda su ka kera ginin, sun caccaki wannan hoton na Odintcova wanda tayi shi ba tare da sanar da kamfanin ba ko kuma neman wata hanyar da zata kare kanta.

Yayin ake wasu shagulgula a benen Cayan, ana samun wasu kwararru da ke samar da hanyar kariya kamar yadda Gizel Daher, darektan kasuwanci da sadarwa ya bayyana a wata takarda da ya saki ranar Juma’a

Babu yadda za ayi ace Ms. Odintcova ba ta da laifi, kuma muna nan mu na sanya matakan tsaro don gudun irin haka ya auku nan gaba,” a cewar Gizel Daher.

Kamfanin ta bayyana cewa za ta dauki matakin shari’a akan matar. Odintcova ta sanar da The National cewa bata da niyyar kara maimaita abinda tayi amma ta ce ya dace ace an biya ta da wadanda su ka yi mata hoton kudin diyya.

Ya kamata a biya mu kudin diyya saboda bayyana hatsarin ginin da muka yi,” a cewar Odintcova ga The National ta wani sako da ta tura ta yanar gizo.

Mun je saman ne ba don yin wani mummunan abu ba, da wani ya lallaba ya halaka kansa ko kuma ya aiwatar da wani ta’addanci.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Dubai, Manjo Janar Khalil Ibrahim Al Mansouri ya sanar da The National cewa sun gayyaceta inda su ka sa ta sanya hannu akan cewa ba za ta sake makamancin hakan ba ta hanyar sa rayuwarta a hatsari

Odintcova ta sanar da jaridar cewa tana mai bayar da hakuri kuma za ta sanya hannu akan takardar da ‘yan sanda su ka tura mata ta yanar gizo.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.