Yadda zaka dawo da katinka na dan kasa idan ya bata ko an sace
Abubuwan da zasu iya sawa a rasa katin dan kasa za’a iya raba su zuwa gida hudu kamar haka:
- Sata
- Faduwa
- Canja suna
- Lalacewa
Canja suna zai iya daukar kuskuren wajen rubuta sunan ko kuma kara suna ko rage suna, duk yana karkshin dai dawo da katin dan kasa:
1. Sata ko kuma 2 Bata.
Idan sacewa akayi ko kuma bata kana bukatar abubuwa kamar haka:
- Takardar yan sanda ta rahoto
- Takardar rantsuwa a kotu
- Takardar shaidar biyan kudi (500)
- Hoto ID.
. Lalacewa
Idan kuma lalacewa yayi kana bukatar abubuwa guda biyu:
- Shaidar lalacewar (ka tafi da lalatancen zuwa ofishin NIN
- Shaidar biyan kudi (500)
4. Canja suna.
Canja suna shima abu biyu ake bukata kamar haka:
- Takakar da take nuna canjin sunan
- Sai shaidar biyan kudi (500 a duk gyara daya).

Yadda ake biyan kudin (katin dan kasa)
Mataki na farko:
Ka ziyarci wannan shafin www.remita.net.
Mataki na biyu:
Sai ka danna inda aka rubuta pay bills.
Mataki na uku:
Zai kawo maka inda za’a tambeyaka me zaka biya sai ka rubuta National identity management commission. Zai ci gaba da kawo maka zabi zabi sai ka cike.
- Bitget Exchange
- Phemex Spot Trading
- Phemex [Review, Sign-Up, and Login Guide]
- Phemex Cryptocurrency Exchange
- Seyi Vibes’ Full Bazuka : A Fresh Wave of Afrobeat
Mataki na hudu:
Sai ka danna inda aka rubuta submit domin biyan kudin, wani shafin zai sake budewa yadda inda zaka fitar da shaidar biyan kudi ta internet RRR, sai ka buga ta (print out).
Mataki na biyar:
Sai ka zabi kalar biyan kudin da kake so:
Zabin biya da ‘kati’.
Zabin biya da ‘lalita’ (wallet).
Zabin biya da ta ‘reshen banki’.
Zabin biya ta ‘turin banki’.
Zabin biya da ‘dalar Amuraka’.
Bayan ka gama zabar sai ka hade ka fitar har invoice dinka ta RRR.
Wannan ita hanayar da zaka bi ka dawo da katin dan kasa bayan ka rasa shi. Domin karin bayani ko tambaya zaku iya biyomu ta wannan hanyar.
Leave a Reply