KARIYA DAGA SIHIRI, TSAFI KO MUGUN BAKI.
- Ka karanta:
“Laa ilaaha illallahu, wahdahu laa shareeka lah, lahul-mulku, wa lahul-hamdu, wa Huwa alaa kulli shai’in qadeer”
kafa 100 bayan sallar asuba.
- Idan kazo kwanciya, Ka karanta Suratul Ikhlas (Sura ta 112), Falaq (Sura ta 113), Nas (Sura ta 114), ka tofa a hannu, sannan, ka shafe a jikinka gaba daya.
Ka yi haka sau 3.
- Ka karanta:
Hasbiyallaahu laa ilaaha illaa Huwa alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-Arshil Azeem”
Kafa 7, da safe da kuma yamma.
- Ka Karanta:
“Bismillaahil lazee laa yadurru ma’asmihi shai’un fil-ardi walaa fis-samaa’i wa Huwas samee’ul Aleem.”
Kafa 3 da safe da kuma yamma.
- Ka rinka cin Dabino guda 7 (irin wanda ake cema ajwa na madina) kullum da safe.
- Ka karanta:
“A’uzu bi kalimaatil-lahit taammaat min sharri maa khalaqa.”
Kafa uku da safe da yamma.
- Ka karanta Amanar rasulu zuwa karshe lokacin da zaka kwanta barci.
(Suratul Baqara ayata 285 zuwa ta 286).
- Ka rinka kwanciya da alwala.
Allah kabamu kariya da kariyarka, sannan ka rabamu daga sharrin azzalumai.
Leave a Reply