Yadda zaku hada maganin karin Kuzari da Karfi a lokacin saduwa da iyali

Har ila yau dai akwai mutanen da suke fama da rashin karfi da kuzarin a lokacin da suke saduwa da iyalinsu, wanda hakan yake haifar musu da damuwa.

To a yau dai munzo muku da wani ingancaccan hadin maganin karin kuzari wanda mai irin wannan matsala zai sami waraka insha Allahu.

Babu makawa bincike ya nuna amfanin da Tafarnuwa da Citta suke dauke da shi ta bangaren taimakawa karfi ga
Namiji.

Domin suna dauke da sinadarin dake
taimakawa jiki wajen samun cikkaken kuzari.

Da farko za’a sami Citta danya mai ashar
kamar guda 1 babba, sai a bare bawon dake bayan ta.

Sannan a samu Tafarnuwa guda daya a bare a debi sili kamar 3 sai a hada da Cittar a daka a turmi, a kawo ruwa kofi daya a zuba a ciki a barshi na tsawon minti 15 sannan a kawo zuma kamar chokali 4 a zuba a juya sosai asha.

Idan kunyi wannan hadin maganin kun sha sai ku dauki kamar tsawon minti 30 kafin a kwanta barci, amma kasha bayan kaci abinci.

Allah ya bada sa’a, Ameen

wasallam Salati.