Yan Bindiga Sun Sace ‘yan Biki A Garin Dutsin-ma NEWS ALL

Yan bindiga sun sace ‘yan biki a garin Dutsin-ma 

Yan ta’adda sun kutsa cikin hedikwatar karamar hukumar Dutsin-ma ta jihar Katsina suka kuma yi awon gaba da yan biki a daren ranar Asabar. 

Kamar yadda Katsina Post ta samu, yan bindigar sun shiga gidan bikin ne dake bayan gidan Yandaka a gidan wani Alhaji Babangida Abdullahi, a daidai

lokacin da yake hidimar aurar da diyar shi. 

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa yan bindigar sun tafi da mata kawayen amaryar da ‘yan uwa akalla su tara (9) cikin su harda uwar bikin. 

Sai dai rahoton da muka samu sun tabbatar da cewa mahaifiyar amaryar yan bindigar sun bar ta a hanya ne sakamakon kasa tafiya da ta yi kuma har ta dawo gida ma. 

Source- Katsina posts