
‘Yan Fim Suna Kokarin Ganin Bayana, Don Sun Maka Ni A Kotu, Saboda Na Ce Suna Bata Tarbiyya, Cewar Dan Jarida Indabawa Aliyu Imam
A daren jiya aka yi sallama da ni bayan na fito ne sai mutumin ya ce daga Kotu ne aka aiko shi waje na da sammaci. Ya ba ni wasu takardu cewa wai wani Mutum mai suna Hamisu Lamido Iyantama ne ya yi kara ta, saboda na yi rubutu kan ‘yan fim na ce suna lalata tarbiyya, kuma Iyantama dan fim din ne, sannan na yi rubutu na nuna rashin jin dadina sanda wani Sanata mai suna Barau Jibril ya raba wa ‘yan fim motoci, babura, kyamarori, kwamfuyutoci da kudade alhalin mabukata suna mutuwa a asibiti saboda rashin kudin magani, wasu na mutuwa saboda yunwa. Sannan ina goyon bayan Gwamna Ganduje ina adawa da Barau Jibril sanda shi Barau din ke takun saka da Baba Ganduje a kungiyarsu ta G7 Wannan shi ne kadai laifina.Bin tafarkin Annabi (SAW) na umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da yaki da rashin tarbiya ya zama laifin da har ake kokarin a ga bayan mai aikata shi.Zan bibiyi takardar sammaci insha Allahu, tana da yawa sosai. Zan san matakin da ya dace na dauka.Allah ya shiga lamuranmu.
Leave a Reply