Jami’an tsaro sun kama daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina (FUDMA) da ya kashe kishiyar mahaifiyarsa, kuma ya karya kafar Mahaifinsa da tabarya.
Dalibin da ke aji uku a Jami’a mai suna Najeeb Umar Shehu, 24, ya yi ta dukan kishiyar mahaifiyarsa, Hajiya Hasiya Galadima, wacce tsohuwar ma’aikaciya ce a gwamnatin jihar Katsina da tabarya har rai ya yi halinsa.
Da yake bayyana abin da ya faru, Mustapha Umar, ya tabbatar da cewa Najeeb ya dade yana barazanar kashe Hajiya Hasiya, saboda yana zargin ta da hannu wajen mutuwar auren Mahaifiyarsa, kuma an sha kai maganar wajen ‘yan sanda, amma ba a dauki wani mataki ba.
Mustapha ya bayyana cewa kafin Najeeb ya je gidan nasu, sai da ya tatul da kwaya, inda ya shiga dakin girki ya dauko tabarya, ya je ya rutsa marigayiyar a daki ya shiga dukan ta, har sai da ya tabbatar rai ya yi halinsa.
Lokacin da mahaifinsa, Alhaji Umar Shehu Balele, wanda ma’aikaci ne a Ma’aikatar Ilimin Jihar Katsina ya ji hayaniya, ya fito da nufin jin abin da yake faruwa, shi ma sai ya buga masa tabaryar ya karya shi a kafa, kuma ya fadi sumamme.
Yayin da aka yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin musulunci ya tanada, shi kuwa Malam Umar yana kwance a asibiti bangaren kula da kashi yake amsar magani.
Jama’ar unguwa ne suka yi wa Najeeb tara-tara suka kama shi suka mika shi ga jami’an tsaro.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa za su gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Leave a Reply