Yan Sanda Sunyi Zanga Zanga Saboda Yan Achaba Suna Kwanaciya da Matansu Na Aure

Akalla jami’an yan sanda 480 ne suka gudanar da zanga-zanga kan zargin rashin biyansu albashin watanni 18 a Osun.

Sun yi tattaki a manyan unguwanni da mahadar Osogbo, babban birnin jihar Osun domin yin zanga-zanga, jaridar The Nation ta rahoto.

A watan Mayun 2021 ne aka rantsar da jami’an yan sandan a hedkwatar rundunar da ke jihar Osun bayan horar da su a watan Afrilun 2021. An kwashe su aiki ne don karfafa tsarin aikin rundunar ta hanyar bayar da bayanan sirri da sauransu.

Jami’an yan sandan da suka yi zanga-zanga sanye da kayan aiki sun hadu a yankin Old-Garage inda suka yi tattaki ta Oke-Fia, Alekuwodo kafin suka mamaye gadar sama na Ola-Iya don ganin an biya masu bukatunsu.

Sun rike kwalayen sanarwa dauke da rubutu daban-daban kamar: ‘A biya mu albashinmu yanzu’, ‘yan achaba suna kwanciya da matanmu’, ‘a biya mu albashinmu na watanni 18, ‘a biya mu’, ‘albashi da alawus dinmu’ da kuma ‘watanni 18 babu ko kwabo’.

Daya daga cikin shugabannin yan sandan da ke zanga-zanga, Constable Tijani Adewale, ya ce duk da rashin biyansu albashinsu sun jajirce kan ayyukansu yana mai cewa a wannan hali da suke ciki jami’an yan sanda uku ne suka mutu a bakin aiki.

Sun yi korafin cewa yan adaidaita da yan achaba sun kwace masu matayensu saboda basa iya daukar dawainiyansu da yaransu, New Telegraph ta rahoto.

Daga bisani, kwamishinan yan sandan Osun Olawale Olokode ya hadu da su a gadar Ola-Iya sannan ya umurcesu da su dakatar da zanga-zangar nan take.

Ya basu tabbacin cewa hukumomin da ya kamata za su shiga lamarinsu don magance kokensu.

Ya ce:

“Kuna kunyata rundunar da zanga-zangarku. Da kamata yayi ku karkata kokenku zuwa kwatas din da dace. Kuna damun zaman lafiyar al’umma da wannan zanga-zanga naku. Idan dai har kuna sanye da wannan inifam din, muna sanya ran ku zamo masu da’a kamar jami’in tsaro.”