YANZU YANZU: An Haramta Jin Wakokin Warr da A Sosa Na Ado Gwanja a Nigeria

YANZU-YANZU: An Haramta Jin Wakokin ‘Warr’ Da ‘A Sosa’ Na Ado Gwanja A Gidajen Rediyo Da Talabijin A Kaf Fadin Nijeriya

Hukumar dake kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ta haramta sanya Waƙar Ado Gwanja ma taken “WARR” a gidajen Radiyo da Talabijin a faɗin ƙasar nan.

A cewar takardar Sanarwar Hukumar ta lura cewa Waƙar ta karade Gidajen radio da Talabijin a faɗin Arewacin ƙasar nan, sannan akwai yiyuwar masu Gidajen kafafen yaɗa labaran basu saurari Waƙar da kyau ba domin tana ɗauke da wasu kalamai na rashin da’a.

Masu karatu mene ne ra’ayinku kan hakan?