Jaridar Rariya hausa ta ruwaito rahoton cewa Hukumar DSS Ta Kama Limamin Masallacin Abduljabbar Bayan An Gan Shi Yana Zirga-zirga A Kusa Da Kotu
Rahotani sun nuna cewa an kama Saifullahi Satatima bayan ganin yana zirga-zirga a kusa da kotu, inda hukumar DSS suke zargin akwai abinda yake kullawa.
Saifullahi shine limamin masallacin Abduljabbar na Sabuwar Gandu.
Kamar yadda aka sani Jaridar BBC hausa ta ruwaito yadda wata Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.
An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola yace an same shi da dukkan laifukan da ake tuhumarsa dasu.
Mun gode da Ziyartar wannan Shafi namu wanda yake kawo maku labarai da dumi duminsu.