YANZU-YANZU| Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kori Sojoji Biyu Da suka Hallaka Sheikh Aisami Damaturu Daga Aiki

YANZU-YANZU| Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kori Sojoji Biyu Da suka Hallaka Sheikh Aisami

Damaturu Daga Aiki Rundinar sojin Nigeria ta kori sojoji guda biyu wadanda ‘yan sanda suka kama da laifin aikata kisan kai da fashi da makami Sune sojojin da suka harbe babban Malamin Musulunci a jihar Yobe Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da yunkurin sace motar Malamin Sojojin masu mukamin Lance Corporals wato Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Gideon

Adamu, amma kafin a koresu daga aiki sai da aka rege musu matsayi zuwa kuratan Sojoji wato Private Laftanar Kanar Ibrahim Abdullahi Osabo shine Mukaddashin Kwamandan Recce Battalion rundina ta 241 dake da sansani a garin Nguru jihar Yobe inda sojojin suke aiki ya gabatar da korarrun sojojin, sannan ya mikasu wa ‘yan sanda domin a gurfanar da su a Kotu Aladu sun kashe ragon layya, tabbas ba zasu tsira ba Muna fatan Allah Ya tabbatar musu da mafi tsananin hukunci Allah Ya karbi shahadar Sheikh Muhammad Goni