Tsawa Ta Fadowa Wata Yarinya A Makarantar Islamiyya A JiharJigawa da Wani Dan Agaji A Katsina

Hon Saleh Shehu Hadejia cewar wata tsawa mai karfi ta fadowa wata yarinya mai suna Maryam Rabiu Garba Kaugama a garin Kaugama dake jihar Jigawa.
Marigayiyar ‘ya ce ga tsohon dan majalistar taraiyya mai wakiltar Malammadiri da Kaugama.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ta je cikin makarantar Islamiyya domin yin karatun Alqur’ani Mai Girma.
Allah Ubangiji ya gafarta mata.
Wata Tsawar Ta Kashe Dan Agaji Duk A Yau:
A wani bangaren kuma wani wakilin namu ya ruwaito daga Nura Rabe Dandagoro cewar wata Tsawar kuma Ta Yi Silar Mutuwar Dan Agaji Addinin Musulunci A Jihar Katsina
“Sakamakon ruwan da aka tafka hade da tsawa ta yi sanadiyyar rasuwar makwabcinmu mai suna Attahiru Abdu, wanda kafin rasuwarsa yana aikin Agaji na Fityanul Islam”.

Leave a Reply