Yaron da ya sha hannu da Gwamna Zulum ya samu kyautar dankareren hoton sa

Wani yaro da yayi farin gani inda yayi musabaha da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana ya Samu kyautan dankareren hoton su da aka dauka ya yin da suke shan hannu da gwamnan Sai dai wasu ‘yan bani na iya suna cewa mutumin da ke cikin ayarin motocin ba Zulum ba ne, mataimakin sa ne saboda alama ta nuna haka“mataimakin gwamna.”

Yaro zai gana da Gwamna Zulum

Mai amfani da shafin Twitter, Governor CBN, Akinsola ya bayyana cewa yaron ya sami hoton da aka zana daga wanda hadimin gwamnan ne ya bashi kuma ana sa ran yaron zai gana da gwamnan nan ba da jimawa ba.
A cikin wani sakon Twitter da ya wallafa a a ranar 2 ga watan Agusta, 2022, Akinsola ya wallafa hotunan yaron tare da dankareren hoton da akayi masa kyauta ride a hannun sa. Jaridar Labarun hausa ta bayyana cewa batada tabbacin ko da gaske gwamna zulum ne a cikin motar wanda har ta kai Yasha hannu da yaron, amma rahotanni sun yi ta yaduwa a shafukan sada zumunta cewa Zulum ya sha hannu da mutanen gari. Wani daga cikin hoton shine wanda aka ba wa wanna yaron inda aka ganshi ride da hoto cikin farin ciki.