Buhari ya ce jami’an tsaro na da hurumin farauta, bibiyar su, da kuma magana da ‘yan ta’adda da yaren da suka fi fahimta.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro da su farauto ‘yan ta’adda a cikin iyakokin Najeriya, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya ce jami’an tsaro na da hurumin farauta, bibiyar su, da kuma magana da ‘yan ta’adda da yaren da suka fi fahimta.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen taron kan hadin kan yan kasa, zaman lafiya da tsaro wanda cibiyar hulda da jama’a da abokan hulda ta Najeriya ta shirya, wanda aka gudanar a Abuja.
Buhari wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce za a fatattaki ‘yan ta’adda daga Najeriya.
Yace, Ya yi alkawarin samun nasarar magance ta’addanci da ‘yan fashin dajj a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa: “Mun umurci sojoji da su murkushe wadanda ke addabar ‘yan kasar, sannu a hankali za’a dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
“A cikin kwanaki biyun da suka gabata, tabbas kun ji labarin adadin ‘yan ta’addan da sojoji suka kashe, da kuma adadin wadanda aka yi nasarar ceto su daga hannun garkuwa da su.
“Dole ne mu kai farmaki ga ‘yan ta’addar, mu nuna cewa babu wata maboya a cikin iyakokin kasarmu.
“Kowannen za a farauta, a bi su kuma a yi magana da su cikin harshen da suke fahimta.”
